Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 6 ga watan Yuni, 2024.
Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ne ke fatan za mu kwana lafiya.
Asalin hoton, Getty Images
Tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles ta yi canjaras da Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya.
Yayin wasan da aka fafata a filin wasa na Godswill Akpabio a jihar Akwa Ibom, ɗan wasan gaba Zwane ne ya fara ci wa Afirka ta Kudu ƙwallo a minti na 29 bayan ya zagaye 'yan bayan Najeriya biyu kuma ya yarɓa ta a ragar Nwabali.
Sai a minti biyu da komawa hutun rabin lokaci Dele Bashiru ya farke wa Najeriya, inda shi ma ya taƙarƙare ya zabga wa Romwen Williams ƙwallo daga yadi na 18.
Ademola Lookman Samuel Chukwueze na Najeriya sun samu damarmakin da suka kamata su cinye wasan, amma ƙoƙarinsu bai kai ba.
Najeriya ce ta fi mamaye wasan musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Da wannan sakamakon, Afirka ta Kudu ta koma mataki na huɗu da maki huɗu, Najeriya kuma ta biyar da maki uku.
Sai a cikin shekara mai zuwa ne Najeriya za ta ziyarci Afirka ta Kudu don buga zagaye na biyu.
Amma a ranar Litinin Najeriya za ta je Ivory Coast don karawa da Benin, yayin da Afirka ta Kudu za ta buga da Zimbabwe ranar Talata.
An raba maki tsakanin giwayen Afirka a harkar ƙwallo da kuma tattalin arziki.
Ademola Lookamn ya ɗaɗa wa Williams ƙwallo kuma da kyar ya tura ta kwana.
Ademola Lookman ya zubar da dama mai kyau a cikin yadi na 18 ɗin Afirka ta Kudu.
Ƙwallo ce suka yi ba ni in ba ka amma sai ya buga ta waje ba tare da wani haɗari ba ga gola Williams.
Terem Moffi ya maye gurbin Onuachu. Sai kuma Onyedika da ya karɓi Ajayi.
Chukwueze ya doko tirke bayan Alhassan ya ba shi wata ƙwallo mai ƙayatarwa.
Dama ce mai kyau sosai, da tuni Najeriya ta shiga gaba ba don tirken sama ba.
Alex Iwobi ya buga ƙwallo ta yi sama da yawa.
Osayi Samuel ya kusa ci wa Najeriya bayan ya ɗaɗa ƙwallo a cikin yadi na 18 – amma sai a hannun Williams
Foster ya maye gurbin Rayners
Samuel Chukuwueze ya maye gurbin Kelechi Iheanacho.
An sako Yusuf Alhassan a madadin Bashiru.
Ɗan wasan tsakiyar Najeriya kuma maciyin ƙwallon, Dele Bashiru, ya kwanta yana nuna alamun ba zai iya ci gaba da wasa ba.
Ko wane mataki mai horarwa Finidi George zai ɗauka?
An bai wa Ngezana na Afirka ta Kudu katin gargaɗi.
An bai wa Mudau na Afirka ta Kudu katin gargaɗi saboda ƙeta.
Bashiru ya farke wa Najeriya ƙwallo minti biyu da komawa hutun rabin lokaci.
Sai da ya bintsire 'yan bayan sannan ya sheƙa ta ragar Williams.
An tafi hutun rabin lokaci yayin da baƙi ke yin nasara 0-1.
Matuƙar Najeriya na son zuwa gasar Kofin Duniya ta 2026 wajibi ne ta farke kuma ta cinye wasan domin kuwa yanzu haka ita ce ta biyar a teburin rukunin.
Tuni Afirka ta Kudu ta ɗare saman teburin sakamakon wannan ƙwallon da Zwane ya ci mata a minti na 29 da take wasa.
Asalin hoton, NFF
Paul Onuachu ya goga wa ƙwallo kai, inda ya kusa farke wa Najeriya. Sai dai Williams ya yi wuf ya rufe ƙwallon.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

You must be logged in to post a comment.