Asalin hoton,
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinkirta dawowarsa daga hutu da kuma jinyar da ya je Biritaniya har sai ranar Lahadi domin ya kara hutawa.
Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce Shugaba Buhari na nan lafiya amma zai dan kara kwanakin hutun nasa.
A makon da ya gabata ne shugaban, mai shekaru 73, ya tafi London domin yin jinyar ciwon kunnen da yake fama da shi bisa shawarar likitocinsa na Najeriya.
Mista Osinbajo ya shaida wa manema labarai a Abuja "Shugaba Buhari yana cikin koshin lafiya kuma a shirye yake ya dawo aiki ranar Litinin da safe."
Farfesa Osinbajo ya ce ya yi magana da Mista Buhari ranar Laraba da daddare.
End of Wanda aka fi karantawa
"Zai dauki kwana daya ko biyu domin ya hutu sannan ya komo aiki a ranar Litinin."
Shugaba Buhari ya bar Najeriya ne bayan ya soke halartar wasu manya-manyan tarurruka a yankin Naija Delta da kuma birnin Lagos.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

You must be logged in to post a comment.