Global site navigation
Na gargajiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Adamawa – Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi magana kan abin da Najeriya take da buƙata.
Atiku Abubakar ya ce Najeriya na buƙatar garambawul cikin gaggawa domin ƴan ƙasa su ci moriyar dimokuraɗiyya.
Atiku ya bayyana hakan ne yin da yake magana a birnin Yola a wajen taron haɗaka a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taron haɗakar wanda aka gudanar a birnin Yola ya samu halartar mambobin jam’iyyun siyasa daban-daban.
Kara karanta wannan
Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai za su zaɓi wanda zai gwabza da Tinubu a 2027
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na jam’iyyar PDP a zaɓukan 2019 da 2023 ya ce abubuwa ba su tafiya daidai a ƙasar nan.
– Atiku Abubakar
Atiku Abubakar ya ƙara da cewa zai yi magana kan batutuwan ƙasa nan ba da jimawa ba kuma zai fayyace matsayinsa na siyasa, inda y roƙi magoya bayansa da su kwantar da hankulansu.
– Atiku Abubakar
Wanda ya shirya taron, Sanata Ishaku Abbo, ya bayyanawa mahalarta taron cewa Atiku shi ne jagoransu a siyasa, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba.
Kara karanta wannan
Shirin fatattakar Tinubu ya samu cikas bayan matsayar sakataren PDP kan haɗakar Atiku
Ishaku Abbo wanda ya sauya-sheka gabanin zaben 2023 ya rasa kujerarsa ne a majalisar dattawa da alkali ya tsige shi, ya ba jam'iyyar PDP nasara a Adamawa.
– Ishaku Abbo
Abbo ya ce kyawawan halayen jagoranci da Atiku ya nuna a lokacin da ya yi mataimakin shugaban ƙasa na tsawon shekaru takwas, sun sanya masu kishin dimokuradiyya suna ƙaunarsa.
Taron ya samu halartar wakilai daga dukkan ƙananan hukumomi 21 na jihar Adamawa, ciki har da masu taimakawa ƴan takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaɓen 2023, Sanata Aishatu Binani.
Ɗaya daga cikin masu taimakawa Binani, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa tana cikin wannan haɗaka.
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi wa shugabannin majalisar dokokin tarayya kaca-kaca.
Atiku ya zargi Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas da rashin gaskiya saboda amincewa da dokar ta ɓacin da mai girma Bola Tinubu ya sanya a jihar Rivers.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
Sharif Lawal Sharif Lawal ma’aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

You must be logged in to post a comment.