Global site navigation
Na gargajiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai tare da jimamin kisan gillar da aka yi wa mafarauta ƴan Arewa a Jihar Edo.
Atiku ya yi kira ga hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike domin doka ta yi aiki a kan waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.
Wazirin Adamawa ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Juma'a, 28 ga watan Maris, 2025.
Kara karanta wannan
Gwamnonin Arewa sun haɗa kai kan kisan Hausawa a Edo, sun shawarci al’umma
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwa da ya fitar, Atiku ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da duka wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan mummunan lamari.
Tun farko, Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa wasu matasa sun hallaka matafiya ƴan Arewa 16 yayin da suke hanyar zuwa Kano domin yin sallah a gida.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a garin Uromi da ke yankin ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas a jihar Edo, yankin Kudu maso Kudancin Najeriya.
Jim kaɗan bayan haka, Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya ba da umarnin fara bincike kan lamarin, kuma ya roƙi al'umma su kwantar da hankula.
Da yake mayar da martani, Atiku Abubakar ya nuna bacin ransa kan wannan mummunan lamarin, ya kuma nemi a yi wa waɗanda aka kashe adalci.
Kara karanta wannan
Kisan ‘rashin imani’ da aka yi wa ‘yan Arewa ya tada ƙura, Kwankwaso ya maida martani
– In ji Atiku Abubakar.
A baya, kun ji cewa madugun Kwankwasiya ya yi Allah wadai da mummunan kisan gillar da wasu mutanen gari suka yi wa ƴan Arewa a jihar Edo.
Rabiu Kwankwaso ya bukaci hukumomin tsaro da su yi cikakken bincike kan lamarin tare da tabbatar da an hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa.
Asali: Legit.ng
Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma’aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al’amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

You must be logged in to post a comment.