An samo ƙarin gawar mutum biyu daga waɗanda kwale-kwale ya kife da su a jihar Naija – BBC

Asalin hoton, NEMA
Hukumar agajin gaggawa ta jihar Naija, ta ce da safiyar ranar Alhamis jami'an da ke aikin ceto mutanen da kwale-kwale ya kife da su ranar Talata sun ƙara samo gawar mutum biyu.
Mai magana da yawun hukumar, Ibrahim Audu Hussaini ya shaida wa BBC cewa "kawo yanzu an samu gawar mutum 18 tun fara aikin. Sannan kuma an ceto mutum 150 da ransu."
Sai dai kuma kakakin hukumar bai faɗi ragowar mutanen da ake nema ba amma ya ce " ana sa ran sun wuce mutun 100."
A ranar Talata ne dai kwale-kwalen ya kia cikin kwale-kwalen lokacin da ya kife a madatsar ruwa ta Jebba a garin Gbajibo da ke ƙaramar hukumar da yammacin ranar Talata.
Kwale-kwalen wanda ya taso daga Mundi zai tafi Gbajibo domin halartar bikin Maulidi cike yake maƙil da mata da ƙananan yara.
Har yanzu dai ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto ƙarƙashin jagorancin hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar da sauran mutane.
Ko a watan Satumban 2023, an samu kwatankwacin irin wannan, inda kwale-kwale ɗauke da fasinja 50 ya kife kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 24 a jihar.
Asalin hoton, Niger state NEMA
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

source

Share and Earn ₦1,000

You must be logged in to post a comment.