Asalin hoton, Getty Images
Wani binciken da BBC ta gudanar ya gano zargin cewa katafaren kamfanin mai na Shell ya yi burus da gargaɗin da aka yi ta yi masa cewa akwai matsala ta rashin gaskiya da ƙumbiya-ƙumbiya da rashawa a game da wani aikin tsaftace yankin da ya gurɓata da mai a kudancin Najeriya.
Kamfanin na duniya da cibiyarsa take a London, tare da gwamnatin Najeriya sun yi ta nanata cewa aikin share man da ya gurɓata muhalli a yankin Ogoni wanda aka fara shekara takwas baya na tafiya da kyau – babu wata matsala.
To amma BBC ta gano cewa an yi ta gargaɗin kamfanin cewa aikin wanda gwamnati ta tsara kuma kamfanonin mai da dama suka samar da kuɗaɗen gudanar da shi, da suka kai dala biliyan ɗaya (fam miliyan 805) yana fama da matsaloli.
Wani da ke sa ido sosai kan abin da ke wakana game da aikin share man ya bayyana shi a matsayin baɗakala da aka ɓarnatar da kuɗi da kuma ta bar mutanen Naija Delta ci gaba da rayuwa da mummunar illar man da ke gurɓata musu muhalli – shekara 13 bayan babban rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya da ya nuna irin illar matsalar gurɓata muhallin da man ke yi.
Kamfanin Shell ya gaya wa BBC cewa: "Yankin da ake aikin har yanzu yana tattare da matsaloli saboda gaggaruman haramtattun abubuwan da ake yi a can kamar satar mai.
"Idan aka samu zubar mai daga cibiyoyin mu nan da nan muke sharewa, kuma mu biya diyya. Idan kuma kwarara ce ta yanayin aiki, ita ma muna biyan diyya ga jama'a da garuruwa.
Ana zargin kamfanin da yin burus da ankararwar da aka yi ta masa ne, a kan rashin gaskiyar da ke tattare da aikin, yayin da za a fara shari'a a babbar kotun London ranar Alhamis kan batun, inda lauyoyi da ke wakiltar kusan mutum 50,000 za su cedole kamfanin Shell ya ɗauki alhakin gurɓata yankin da mai a tsakanin1989 da 2020.
Mutanen garuruwan sun ce kwararar man ta sa sun rasa tsaftacaccen ruwa, ba sa iya noma da kamun kifi kuma tana haddasa musu illa sosai ga lafiyarsu.
Shell, wanda yake ta ƙoƙarin sayar da kadarorinsa a Najeriyar domin mayar da hankali kan haƙar mai a teku da iskar gas a tudu ya ce zai yi duk abin da zai iya ya kare kansa.
Kamfanin ya ce ba abin da ya yi na ba daidai ba – yana mai danganta gurɓatar muhallin da mai da ƙafar-ungulu da masu satar man da masu tace shi ta haramtacciyar hanya, abin da ya ce ba alhakinsa ba ne.
BBC ta ziyarci yankin da abin ya shafa a Naija Delta inda kamfanin na Shell, kamfanin 'yankasuwa na mai da iskar gas mafi girma a ƙasar ya gano ɗanyen mai shekara 68 da ta wuce a ƙasar.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla gangar ɗanyen mai miliyan 13 ko tan miliyan 1.5 ne ya zube tare da gurɓata yankin tun 1958, a aƙalla karo 7,000.
Zubewar ta jefa iyalai da dama cikin damuwa game da lafiya da kuma hanyoyin gudanar da rayuwarsu.
Wata mata Grace Audi, mai shekara 37, tana tare da abokin zamanta da kuma 'yarsu mai shekara biyu a garin Ogale, inda aka samu zubar man aƙalla sau 40 daga kayan aikin kamfanin na Shell – kamar yadda kamfanin lauyoyi na Leigh Day, da ke Birtaniya wanda ke wakiltar al'ummomin ya ce.
Matar da iyalanta da kuma maƙwabtansu ba su da hanyar samun ruwa mai kyau da rijiyar burtsatsensu – abin da ya sa dole suke sayen ruwan da za su sha da girki da wanki a kullum na aƙalla naira 4,500 (dala 3, ko fam 2.40), a yankin da ƙudin da yawancin mutane ke samu a kullum bai kai dala 8 ba.
Labarin haka yake ga yawancin al'ummar wannan yanki na Ogoni
Paulina Agbekpekpe ta gaya wa BBC cewa a da bishiyoyi da ciyayi ne koraye shar suka kewaye yankinsu, garin Bodo – al'ummar da ba sa daga cikin waɗanda ke cikin wannan shari'a ta ranar Alhamis.
Ta ce a da ba irin dabbar ruwa da kifi da ba su da shi a ruwan garinsu. ''Amma yanzu wannan gurɓatar man ta lalata kusan komai a ko'ina,'' in ji matar mai shekara 50 da 'ya'ya shida.
Ta ƙara da cewa a da tsawon shekaru aru-aru iyaye da kakanni da kuma a nan kusa-kusa iyalanta sun dogara ne da kamun kifi, kafin wata mummunar kwararar mai da ta faru shekara goma ba ya.
"Yawancin yara sun kamu da cutuka a dalilin shan ruwa. Yawanci kuma sun mutu. Na rasa 'ya'ya takwas. Mijina ba shi da lafiya.
"Saboda an lalata mana hanyar rayuwarmu, al'ummar Bodo a yanzu suna cikin yunwa da wahala.
Shirin kare muhalli na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNEP) ya wallafa wani babban bincike da ya yi a kan tasirin gurɓata muhalli a kan yankin.
Hukumar ta gano mutanen wani gari a yankin na Ogoni na shan ruwan da ya gurɓata da wata guba ( carcinogen ) wadda yawanta a ruwan nasu ya ninka 900 sama da yawan da hukumar lafiya ta duniya ta amince da shi. Haka kuma an samu wannan guba da kuma ta benzene a cikin abubuwan da aka ɗiba a jikin mutanen yankin domin gudanar da bincike na lafiya.
Haka kuma hukumar ta gano cewa wuraren da kamfanin man ya ce ya share man da ya zuba ya gurɓata su, har yanzu a gurɓace suke kuma tsarin da suke bi wajen gudanar da aikin bai kai wanda ya kamata a ce na ƙa'ida ba.
Rahoton ya nuna cewa aikin tsaftace yankin zai iya ɗaukan shekara 25 zuwa 30.
A shekara ta 2012 gwamnatin Najeriya ta tabbatar da hakan amma kuma ba a fara sharewar ba har sai bayan da wata sabuwar gwamnatin ta ƙaddamar da shi a watan Disamba na 2016.
Kamfanonin mai ciki har da na gwamnatin Najeriya, NNPC da Shell ne suka bayar da dala miliyan 350 domin aikin.
To amma kuma BBC ta ga takardun da aka aika da ke nuna an gargaɗi wakilan kamfanin na Shell da gwamnatin Najeriya a kan abubuwa da dama na almundahana a kan aikin.
Wani mutum da ke da masaniya gane da aikin ya yi wa BBC ƙarin bayani bisa sharaɗin sakaya sunanansa saboda abin da zai iya biyo baya.
"Abu ne da kowa ya sani abin da muke yi ba na gaskiya ba ne.Yawancinsamuna yi ne domin yaudarar mutanen Ogoni.
"Dabara ce da ake yi ta yadda za a zuba kuɗi sosai a aikin, kuma 'yansiyasa da sauran mutanen gwamnati ne za su kwashe kuɗin." In ji mutumin.
Zargin da ake yi a kan aikin share man ya haɗa da:
Takardu da lokuta da dama na rahotanni da rubuce-rubuce da BBC ta gani sun nuna yadda aka riƙa ankarar da kamfanin na Shell da gwamnati kan rashin gaskiyar da ke tattare da aikin.
BBC ta nemi ji daga shirin share man (Hyprep) da kuma gwamnatin Najeriya, amma ba su ce komai ba.
To amma binciken BBC ya gano cewa akwai shedun da suka tabbatar kamfanin Shell ya san da wannan matsaloli.
Shell ya gaya wa BBC cewa: "Hyprep hukuma ce ta gwamnatin Najeriya da ta ƙunshi manyan ministoci da manyan jami'an gwamnati da kuma wakilan al'ummomi biyar da ƙungiyoyin farar hula da kuma wakilin Shellguda ɗaya kawai.''
Asalin hoton, AFP
Wannan ba shi kaɗai ba ne aikin share mai a yankin Ogoni da ake zargin yana cike da almundahana.
A 2015, Shell ya amince ya biya fam miliyan 55 don share mai da ya zuba bayan wata zuba da aka samu mummuna har biyu a 2008, daga kayan aikin kamfanin a yankin Bodo.
Kamfanin ya ce, an biya kashi 98 cikin ɗari na kuɗin aikin sharewar wanda ya kasance na haɗin guiwa tare da wakilan ɓangarori masu ruwa da tsaki.
To amma kuma BBC ta ziyarci yankin inda ta ga ɗanyen mai na tsatsowa daga ƙasa kuma yana yawo a kan ruwa.
Kamfanin Shell da BMI sun kafe cewa duk wani abu na gurɓatar mai da aka gani a yankin sakamakon masu satar mai ne.
"Akwai shirin sake kiran ɗankwangilar da ya yi aikin sharewar ya dawo ya yi aikin yadda yarjejeniya ta tanada," in ji Boniface Dumpe, darekta a kamfanin BMI, kamar yadda ya gaya wa BBC.
Shell ya ce yana ɗaukar ƙwararan matakai domin hana zubar mai ta hanyar ayyukan masu satar mai.
Zargin almundahanar aikin share man ya taso ne yayin da kamfanin Shell
ke shirin sayar da reshen kamfanin na Najeriya, SPDC, ga Renaissance Africa, wanda haɗaka ne na kamfanonin cikin gida da na waje.
Wasu al'ummar yankin na Ogoni na zargin kamfanin man na Shell da neman kauce wa tsaftace yankin yadda ya kamata daga gurɓata shi da ake zargin ya yi.
Haka kuma sun yi zargin cewa kamfanin har yanzu zai iya cin gajiyar yankin ta hanyar kasuwancin man da aka samu daga yankin a nan gaba.
''Ayyukan duk kamfanin da amfani da bututan man suka koma wajensa za su kasance da tasiri sosai a kan rayuwar al'ummar, '" in ji Joe Snape, na kamfanin lauyoyi na Leigh Day, a hirarsa da BBC.
Ya ce ba a san yadda lamarin zai kasance da kamfanin Renaissance [Africa] ba nan gaba. Domin idan da Shell ne aƙalla an san su za a ɗora musu aihakin abin da ya faru.
Man fetur da iskar ne ke samar wa da Najeriya kashi 90 cikin ɗari na arzikinta, yawanci kuma daga yankin Naija Delta ne.
Al'ummar yankin waɗanda babban abin da suka dogara da shi wajen rayuwa shi ne noma da su sun gaya wa BBC cewa tun bayan da aka gano mai, yankin nasu ya zama saniyar-tatsa ga manyan kamfanonin mai da ɓarayin mai da kuma gurɓatattun 'yansiyasa.
Mutanen sun ce su ba su ga amfanin man ba, sai dai wahala kawai – kamar Patience Ogboe wadda ta ɗora alhakin rashin samun amfanin gona mai kyau kwanan nan a kan malalar mai.
Ta ce a da idan ta yi noma takan samu isasshen abincin da za ta ci da iyalanta har ma ta sayar da wani – amma a 'yan shekarun da suka gabata ta ce ba ta samun komai. kamar yadda matar mai shekara 42 ta sheda wa BBC.
© 2025 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.

You must be logged in to post a comment.